Har Yanzu Ana Neman Sojoji 101 Da Ake Zargin Sun Tsere Tun Bayan Harin Boko Haram


Rahotanni na tabbatar da cewa akalla sojoji 101 ne suka bata tun bayan kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai garuruwan Marte da Dikwa da ke Jihar Barno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar daga sojojin da suka bata akwai hafsoshi 12 da kuma kananan sojoji 86 kamar yadda wasikar da Kanar A.O. Odubuyi ya rubuta a madadin Kwamandan rundunar dake yaki da boko haram ta Lafiya Dole dake Maiduguri.

Wasikar ta ce daga cikin sojojin akwai masu rike da mukamin Manjo guda 3 da Kaftin guda 3 da Laftanar guda 6 da Saje-Saje guda 3 da kuma kananan sojoji 89.

Wasikar ta bayyana wadannan jami’ai a matsayin wadanda suka gudu daga wurin aiki lokacin da mayakan boko haram suka kai hari a Sabuwar Marte da Dikwa.

Wasikar sojin ta bukaci bayyana wadannan dakaru a matsayin wadanda suka gudu daga aiki, yayin da ta bada umurnin rufe asusun ajiyar su da kuma kamo su ko yi musu rakiya zuwa Cibiyar sojin duk inda aka gan su.

Jaridar ta ce Daraktan yada labaran sojin Janar Mohammed Yerima bai yi karin haske game da labarin ba, inda yake cewa idan suna da bayanin da ya dace duniya ta sani za su yi magana akai.

A ranar 14 ga watan Fabarairu mayakan boko haram suka kai hari Marte inda suka karbe iko da garin kafin kai hari Dikwa ranar 19 ga wata, abin da ya sa shugaban sojin Janar Attahiru Ibrahim ya ziyarci dakarun inda ya basu umurnin sake kwato garin da kauyukan dake kusa da shi.

Ziyarar shugaban sojin ya karfafawa sojin guiwar sake kwace iko da Marte da wasu garuruwa dake yankin.


Post a Comment

0 Comments