Jami'ar Gwamnatin Tarayya Da Ke Gusau Ta Karyata Labarin Kai Mata Harin 'Yan Bindiga


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau 

Shugabannin Jami'ar gwamnatin Tarayya dake Gusau (FUG) sun karyata labarin  shafukan sada zumunta wanda ke cewa, 'yan Bindiga da suka kai hari a harabar jami'ar a ranar Alhamis da ta gabata.

 Jami’in yada labarai na jami’ar, Malam Umar Usman ya  bayyana haka a takardar da ya aanya ma hannu ya raba wa manema labarai a Gusau.

UMAR Usman ya bayyana cewa  labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta game da harin ‘yanbindiga, zuki tamallau ce abin nufi karya ne tsagwaronta.inji Jami'n yada labaran.  

 "Hukumar Jami’ar  gwamnatin Tarayyar  tana  sanar da jama’a cewa, labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na cewa’ "yan fashi sun mamaye harabar Jami’ar da ke kan hanyar  Funtua a ranar Alhamis, 4 ga Maris, 2021 ba gaskiya ba ne .

 Umar Usman ya ce,lamarin ya faruwa ne sakamakon firgitar da daliban su kayi sakamakon samun labarin  sace 'yan matan GGSS Jangebe da sauran batutuwan da suka shafi rashin tsaro a jihar ta Zamfara .

 “Lokacin da daliban suka hangi wasu Fulani maza da suka dawo daga wani biki sai suka  firgita hakan yasa suka fantsama don kare lafiyar su.

 “Don haka Jami’ar ta yi Allah wadi da  yadda mutane ke son yada labarai ba tare da tabbatar da gaskiyar abuba.


 "Hukumar Jami"ar ta kuma gargadi ma'aikata da dalibai game da tura sakonnin sada zumunta kamar yadda aka samu ba tare da bin diddigin yadda ya kamata ba.

Umar ya kara da cewa,tun kafuwar jami'ar a shekarar 2013 ba a taba samun wata barazanar tsaro ba.

 "An kuma yi kira ga ma'aikata da dalibai da su kwantar da hankulansu kuma su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum inji Jami'n yada labaran na jami'ar Umar Usman.

Post a Comment

0 Comments