Jami'ar Maryam Abacha Ta Sanya Wa Babban Titin Jami'ar Sunan Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo

 
Hukumar gudanar da Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ta sanya wa babban titin Jami'ar sunan Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo, wanda Allah ya yi wa rasuwa makon da ya gabata bayan gajeruwar rashin lafiya. 


Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo ya kasance matashi kuma dan uwa ga Shugaban rukunin Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya rasu a Sabon Layi Kara dake karamar Hukumar Gwarzo a jihar Kano. 


Shugaban rukunin Jami'o'in MAAUN da Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo shi ne ya bayyana hakan a yayin addu'ar bakwai na rasuwar Marigayin wanda ya gudana a ranar Lahadin 28 ga Fabarairun 2021 a Sabon Layi Kara dake karamar Hukumar Gwarzo. 


Farfesa Gwarzo ya ce Hukumar gudanar da Jami'ar ta zabi ta sanya sunan Marigayin a babban titin Jami'ar ne domin wanzar da sunan. Inda yanzu aka sanyawa babban titin suna da 'Naziru Yusuf Gwarzo Street'. 

Ya bayyana rasuwar dan uwan na shi a matsayin abu da ya jijjiga shi, kuma ya daga masa hankali, inda ya ce tabbas ya rasa dan uwa nagari kuma abin dogaro. A cewarsa, Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo mutum ne mai son zumunci, inda koyaushe yake karfafa matasa musamman a garinsu da su bai wa ilimin zamani da na addini muhimmanci, inda ya kara da cewa har wala yau mutum ne mai saukin kai. 

Ya kara da cewa; "Naziru mutum ne da ya taba shaida min cewa yana son wani daga cikin iyalinmu ya zama kamar Adamu Gwarzo. Inda na yi masa alkawarin taimaka masa domin ganin ya zama kamar Ni, amma cikin ikon Allah abin da Allah ya kaddara zai auku ke nan", ya lurantar. 

Ya yi addu'a da nufin Allah ya jikan mamacin ya sanya aljannah Firdaus ce makoma. Ya kuma bai wa iyali hakurin jure rashin da aka yi. 

A bangare guda kuma, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya tabbatarwa da al'ummar Sabon Kayi Kara cewa gidauniyyarsa ta Adamu Abubakar Gwarzo ta shirya domin zabar wadanda suka cancanta daga mutanen garin domin su yi karatu a Jami'ar kyauta. Sannan ya ce gidauniyyar har wala yau za ta biyawa wadanda suka kammala Sakandire jarabawar JAMB tare da nema musu gurbin karatu a Jami'o'i daban-daban. 

Ya tabbatar da cewa; "babban burina shi ne nan da shekara goma kauyen Sabon Layi Kara ya zama yana da mafi yawan mutanen da suka kammala Jami'a tare da samar da ayyukan ci gaba". 

Ya kara da cewa; "muna da shirin horas da mata 100 a bangarorin sana'o'i daban-daban tare da ba su jari da za su fara kasuwancinsu", inji Farfesa Adamu Gwarzo. 

A karshe ya yi alkawarin kammala Babban ginin Jami'ar ta MAAUN dake Gwarzo domin bai wa matasan dake yankin damar samun ilimin Jami'a. 


An kaddamar da babban titin Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo ne da yammacin ranar Lahadi 28 ga watan Fabarairun 2021 a wani takaitaccen taro da aka gudanar. 

Post a Comment

0 Comments