‘Katin Shaidar Rigakafin Korona Zai Zama Sharaɗin Fita Daga Nijeriya’

 

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona a Nijeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya ƙasashen waje.

Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Ƙasa yau Asabar jim kaɗan bayan an yi wa Buhari da Osinbajo allurar rigakafin.

Ya buƙaci 'yan Najeriya da su ƙoƙarta domin yin rigakafin da zummar kare kansu daga cutar, wadda tuni ta halaka mutum kusan 2,000 a ƙasar.

"Yin ɗari-ɗari da allurar wajibi ne a daina shi domin kuwa maganar gaskiya ita ce, nan gaba kaɗan babu wanda zai fita daga ƙasar nan ba tare da ya nuna shaidar an yi masa ba," in ji Boss Mustapha.

"Ban tabbatar ba, amma na ji tuni wasu ƙasashe suka fara dakatar da karɓar baƙi, ciki har da na ibada, idan ba su da shaidar rigakafin."

Ya ƙara da cewa Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo sun gabatar da kansu ne a fara yi musu rigakafin domin su tabbatar wa da 'yan ƙasa cewa ba ta da wata illa.

-Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments