Kotun Koli Ta Wanke Dauda Lawal, Ta Ce EFCC Ta Maida Masa Kudaden Da Ta Kwace

Dr Dauda Lawal

Daga Muhammad Farouk 

Kotun koli a ranar Juma’a ta bai wa Hukumar yaki da rashawa wato EFCC, umurnin maida naira biliyan Tara da ta kwace a hannun tsohon Daraktan Bankin ‘First Generation Bank’, Dauda Lawal. 

A hukuncin da mutum biyar na kotun karkashin mai shari’a Muhammad Lawal Garba ta yanke, ta yi watsi da daukaka karar da EFCC ta yi kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yi. Inda kotun ta ce hukuncin da babban kotun tarayya ta yi na sauraren karar Hassan, J da ya gabatar a lamba FHC/L/CS/13/2017 a ranar 16 ga watan Fabarairun 2017, an jinginar da shi gefe. 

“Umurnin kwace naira biliyan tara da miliyan tamanin (N9,080,000,000.00) da aka yi aka mikawa gwamnatin tarayyar Nijeriya, shima an jingine hukuncin. A don haka muna bayar da umurnin wadannan kudade (N9,080,000,000.00) a mayarwa da wanda ya gabatar da kara ba tare da bata lokaci ba”, inji kotun koli.  

Hukuncin da kotun daukaka kara dake Legas ta yi a shari’a mai lamba CA/LAG/CV/480/2019 DAUDA LAWAL V. EFCC & ANOR a ranar 25 ga Maris din 2020, kotun kolin ta tabbatar da hukucin a lamba SC.212/2020, EFCC v. DAUDA LAWAL.

Hukuncin ya karkare da cewa dole ne maida wa Dr Dauda Lawal kudaden da aka kwace a hannunsa na naira biliyan Tara da miliyan Tamanin ba tare da bata lokaci ba. 

A cikin watan Mayun 2016 ne, EFCC ta shigar da karar Lawal bisa zarginsa da halasta haramtattun kudi tare da samun kudaden ta haramtaccen ayyuka. 

 A ranar 7 ga watan Oktoban 2020, Babban kotun tarayya a Legas, ta sallame shi tare da wanke Dr Dauda Lawal bisa zarginsa da halasta haramtattun kudi, karbar kudade ta hanyar da ba su dace ba daga haramtattun ayyuka, da sauran zarge-zargen da EFCC ke masa a lamba ta FHC/L/419C/2018 FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA V. DAUDA LAWAL. 


Post a Comment

0 Comments