Ku Kwantar Da Hankalinku Ba Za A Kara Kudin Fetur Ba –NNPC

….. Ta gargadi masu boye man fetur 

Daga Muhammad Farouk

Sabanin rahotannin da ake yadawa na cewa akwai yiwuwar a kara kudin man fetur a fadin kasarnan, Kamfanin man fetur na kasa, NNPC ya tabbatar da cewa kowa ya kwantar da hankalinsa ba za a kara kudin man fetur din a cikin watan Maris din 2021. 

NNPC ta tabbatar da hakan ne a cikin sanarwar manema labarai da Babban Manaja, kuma shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin, Dr. Kennie Obateru ya fitar, inda ya ce  kamfanin na su suna mai bayar da tabbacin cewa ba za a kara kudin man fetur din ba a Maris ko don ka da su bata yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kungiyar kwadago da wadansu masu ruwa da tsaki a bangaren wanda ya ce idan aka yi karin zai jefa Talaka cikin wahala.

NNPC har wala yau sun gargadi bangaren masu kasuwancin man fetur din (PPM) da ka da su kara kudin fetur din ko su rika boye shi domin haifar da matsalar rashin man fetur din domin sanya Talakan Nijeriya cikin wahala. 

Kamfanin har wala yau ya ce yana da mai isasshe da zai ishi kasar har na tsawon kwana 40, inda suka shawarci masu motoci da ababen hawa da su kwantar da hankalinsu ka da su daga hankalinsu. 

A karshe NNPC ta yi kira ga masu hannu wajen lura da farashin man fetur din da su sanya ido da masu kasuwancin mai din, tare da sanya takunkumi ga duk wanda aka samu yana boye mai din ko kara farashi. 


Post a Comment

0 Comments