Ku Saki Shaikh Zakzaky Ko Allah Ya Tausaya Mana -Sakon Harkar Musulunci Ga Buhari


Daga Wakilinmu

Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky sun nemi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da su saki jagoransu ko kasar ta samu saukin fitintinun da yake addabarta. 

Mabiya Shaikh Zakzaky din sun bayyana hakan ne a wata takardar manema labarai da Shaikh Abdulhamid Bello Zariya ya sanyawa hannu kuma aka raba a Zariya wanda MADOGARA ta samu kwafinta a yau Juma'a. 


Shaikh Abdulhamid Bello ya fara da cewa; "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN! Lallai daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma! A yayin da muke wannan fitowar a yau, kwanaki 1913 ke nan gwamnatin Buhari tana tsare da Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky. Wannan wane irin zalunci ne a ce yau shekaru sama da biyar ana tsare da bawan Allah, ba tare da an tabbatar da laifin da ake zargin sa da aikatawa ba? Wannan wane irin zalunci ne a ce ana tsare da Jagoranmu, bayan an kashe masa ’ya’yansa da dimbin mabiyansa sama da dubu guda? Wannan wane irin zalunci ne a ce ana ci gaba da tsare Jagoranmu, alhali wadanda suka yi wannan kisan suka kuma binne wasu daga cikin wadanda suka kashe a rami guda a makabartar da ke Mando Kaduna ba a kama su an tuhume su da kisa ba?" Ya tambaya. 

Ya ci gaba da cewa; "Har ila yau, wannan wane irin zalunci ne a ce ana tsare da Jagoranmu, alhali yana fama da guban burbushin albarusai a jikinsa yau shekaru sama da biyar? Wannan wane irin zalunci ne ana tsare da Jagoranmu alhali  a watan Sha’aban din nan zai cika shekaru saba’in da haihuwa a duniya? Wannan wane irin zalunci ne a ce ana tsare da Jagoranmu bayan an kona Yayarsa da ranta a gidansa da ke Gyallesu shekaru biyar da suka shude? Wannan wane irin zalunci ne ana tsare da Jagoranmu alhali komai na gidansa an sace, hatta kasar ginin gidan gwamnati ta kwashe yau shekaru biyar da suka shige?" Ya tambaya. 

Ya kara da cewa; "Sannan wannan wane irin zalunci ne ana tsare da Jagoranmu, alhali matarsa, Malama Zeenah Ibrahim ma an hahharbe ta, kuma suna tsare tare alhali ba a yi mata magani ba? Wannan wane irin zalunci ne ana tsare da Jagoranmu alhali Cibiyar Musulunci, Husainiyya Baqiyyatullah da ya gina ta an rusa ta, gwamnati ma na ikirarin ta kwace wurin? Hakika ko a iya nan muka tsaya kowa ya san an zalunci Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky, zaluncin da ba a taba yi wa wani a kasar nan da jama’arsa ba!" Ya lurantar. 

Ya nusasshe da cewa; "To, ba fa za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa! Allah ba ya son zalunci da azzalumai ma’abotansa. Don haka muna kara yin kira da kakkausar murya ga gwamnatin Buhari da ta sakar mana Jagoranmu! To, don me ma ba za ta sake shi ba alhali a kan idonta wani Alkalin babbar kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke hukuncin cewa a sake shi tunda babu wata dokar kasar nan da ma wata dokar kasa da kasa da ta sahhale a ci gaba da tsare shi? Ai a sarari yake cewa ci gaba da tsare Jagoranmu da ake yi da sunan yana fuskantar wata shari’a, karan tsaye ne ga hakkokinsa na Dan Adam da tsarin mulki ya bai wa kowane Dan kasa". 

Muna tuni ga gwamnatin Buhari da jama’ar kasar nan cewa, su sani Allah ba azzalumi ba ne, kuma zai yi sakayya ga wanda aka zalunta tun a nan duniya, balle kuma in an je lahira. Duba da irin matsalolin rashin tsaro da rasa rayuka da ake ta fama da shi a duk fadin kasar nan, musamman ma a nan Arewa, ya kamata jama’ar kasa su duba baya su ga wane irin mugun kuskure wannan gwamnatin ta Buhari ta tafka da kisan jama’a ke faruwa a cikin kasa? In ko har aka duba baya din, za a ga cewa ba wani kuskure babba da gwamnatin nan ta tafka fiye da zaluntar Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky, kuma take ci gaba da yi. Da ma Hausawa sun ce “Alhaki kwikwiyo ne, mai shi yake bi.”

"Har yanzu muna ganin lokaci bai kure wa wannan gwamnatin ba na ta gyara kuskurenta. Wajibinta ne ta saki Jagoranmu Shaikh Zakzaky da ta zalunta, ta kuma nemi hanyar yin adalci kan kisan kiyashin da ta yi a Zariya da abin da ya biyo ba. Gwamnatin nan ita ta nuna wa ’yan kasa cewa ran Dan Adam ba a bakin komai yake ba, sa’ilin da ta aiwatar da kisan mutane sama da duba, kuma ta yi fuska, kamar ba ta yi ba. Ai da da farko ma ta musa cewa ta yi kisa, daga baya ne ta yi ikirarin ta kashe tare da binne ’yan’uwa musulmi 347 a wawakeken rami da talatainin dare don kar duniya ta shaidi wannan ta’annuti", ya lurantar. 

Ya karkare da cewa; "Mu kam ba za mu gaji da fitowa don neman hakkin Jagoranmu Shaikh Zakzaky da ’yan’uwa sama da dubu da gwamnatin Buhari ta kashe ba, madamar ba a yi adalci an sake shi da sauran ’yan’uwa musulmi da suke tsare ba. Za mu ci gaba da yin duk wata mai yiwuwa don ganin hakkakuwar hakan, komai runtsi. Aminci ya tabbata ga masu bin gaskiya". 

Post a Comment

0 Comments