Kungiyar IAMA Ta Duniya Ta Bai Wa Farfesa Gwarzo Mukami

 

                                                        Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo

 

Kungiyar gudanar da ilimi ta duniya wacce aka fi sani da ‘International Academic and Management Association (IAMA)’ a turance ta bai wa shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo mukamin zama memba a cikin masu bada shawarwari wajen gudanar da kungiyar wanda mukamin na shi ya fara aiki daga 5 ga watan Maris din 2021.

Sanarwar bai wa Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo mukamin na dauke ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 5 ga Maris din 2021, wanda shugaban kungiyar IAMA kuma wanda ya kafa kungiyar, Dr. Bikash Sharma ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai kwafin takardar a yau Asabar a Kano. 

Takardar mukamin


Takardar wacce aka yi mata kanu da ‘Sanya ka cikin masu bada shawarwari daga 5 ga Maris din 2021’, ta bayyana cewa an cimma shawarar ba shi mukamin ne bayan zaman da ya gudana a tsakanin kwamitin amintattun kungiyar wanda suka gudanar a ranar 20 ga watan Fabarairun 2021 mai dauke da lamba 002/05032021, inda suka ce an cimma matsaya baki daya ba tare da fuskantar wani kalubale ba a tsakanin masu zaman, inda suka yanke shawarar ba shi mukamin kasancewa memba a cikin masu bada shawarwari wanda mukamin zai fara aiki daga 5 ga watan Maris din 2021.

A yayin da suke taya Farfesa Abubakar-Gwarzo fatan alheri da samun nasara a mukamin da aka ba shi, kungiyar IAMA ta ce tana fatan zai kawo ci gaba a tafiyar tare da fatan ganin ya bada gudummawa wajen ayyukan kungiyar. 

 

Kungiyar IAMA

 

“baki dayan masu gudanar da ‘International Academic and Management Association’ suna mai farin cikin kasancewarka cikinmu, muna fatan hakan zai sanya kasancewarka cikin ayyukan IAMA tare da fadada ci gaban ayyukanta a fadin duniya”, inji takardar. 

 

Karanta wannan labarin; Jami'ar Maryam Abacha Ta Sanya Wa Babban Titin Jami'ar Sunan Marigayi Naziru Yusuf Gwarzo  

Post a Comment

0 Comments