Lantarki Ya Dawo A Maiduguri Bayan Kwashe Wata Biyu Ba Wutar

Jaridar Dimokuradiyya ta labarto cewa; al’ummar garin Maiduguri sun cika da murna bayan da wutar lantarki ya dawo a garin da yammacin ranar Laraba bayan kwashe wata biyu babu wutar lantarkin.

Rahotanni sun nuna cewa garin ya fada halin rashin wutar ne bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka tarwatsa na’urorin da ke sada wutar a garin wanda ke titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Wadansu daga wadanda majiyarmu ta samu damar tattaunawa da su sun jinjinawa hukumar bada wutar lantarkin ta Nijeriya, TCN, da kuma Kamfanin dake raba lantarkin ta Yola, YEDC, da gwamnatin Borno bisa dawo da wutar lantarkin.

Sun ce sun cancanci jinjina musamman ma ma’aikatan TCN, da kuma sojojin da suka ba su tsaro a yayin gudanar da aikin gyaran wutar lantarkin. Wanda suka ce har kusan harin bom aka yi nufin kai musu a yayin gyaran wutar.

Har wala yau sun jinjinawa Gwamna Babagana Zulum na Borno, bisa taimakon da ya bada wajen ganin an gyara wutar lantarkin.

Post a Comment

0 Comments