Mahaifin Daya Cikin Daliban Da Aka Sace A Kaduna Ya Rasu


Mahaifin daya daga cikin daliban kwalejin gandun daji dake Afaka a Kaduna, ya riga mu gidan gaskiya, mutumin mai suna Ibrahim Shamaki, mahaifin wata daga cikin daliban da ‘yan bindiga suka sace ne kwanaki da suka wuce, dalibar mai suna Fatima Ibrahim Shamaki, tana cikin hoton bidiyon da ‘yan bindigar suka saki a shafukan sada zumunta.

Mahaifin daya daga cikin daliban kwalejin gandun daji dake Afaka a Kaduna, ya riga mu gidan gaskiya, mutumin mai suna Ibrahim Shamaki, mahaifi wata daga cikin daliban da ‘yan bindiga suka sace ne kwanaki da suka wuce, dalibar mai suna Fatima Ibrahim Shamaki, tana cikin hoton bidiyon da ‘yan bindigar suka saki a shafukan sada zumunta.

A cikin kwanakin nan dangi wadanda aka sace din sun yi ta nuna rashin jin dadinsu ga abinda suke zargin halin ko-in-kula ne da gwamnatin ta yi da ‘yan uwansu da ake tsare da su, inda suke rokon gwamnatin ta yi duk abinda za ta iya don ceto daliban. Zuwa yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce komi game da lamarin.


-Rahoton LEADERSHIP A YAU


Post a Comment

0 Comments