Mai Digiri Biyu Ya Koma Sana'ar Jari Bola A Legas


Daga Muhammad Farouk

Wani matashi mai suna Sirajo Yazid ya kama sana'ar Jari Bola. Bayanai sun nuna cewa matashin na sana'ar a garin Ikorodu dake jihar Legas. 

Matashin wanda ya yi digirinsa na farko a bangaren sanin tarihi (History) daga Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua dake Katsina wanda ya kammala a shekarar 2015, sannan kuma ya yi digirinsa na biyu ne a bangaren 'Development Studies' daga Jami'ar Bayero dake Kano wanda ya kammala a 2019.

Kuma ya gudanar da hidimar kasarsa, inda aka bashi shaidar kammalawa a shekarar 2016 kamar yadda MADOGARA ta labarto. 

Matashin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwara ya mutu da kafafunsa da ya rayu a kan 'yan yatsunsa. Inda ya kara da cewa; "gwara na yi datti na gamsu da abin da nake. Da na kasance cikin tsafta amma ina fama da yunwa. Nagodewa kasar da ba ta mutunta masu ilimi", ya rubuta. 

Yazid Sirajo dai dan garin Karofi ne dake karamar Hukumar Dutsinma a jihar Katsina. 

Post a Comment

0 Comments