Masarautar Zazzau Ta Nada Dan Uwan Zakzaky Modibbon Zazzau

Daga Wakilinmu 

A ranar Asabar 6 ga watan Maris 2021, Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya yi wa Sheikh Sani Yaqoub, shugaban kungiyar Izala na karamar Hukumar Zariya nadin sarautar Modibbon Zazzau. 

Shi dai Sheikh Sani Yaqoub Dan uwa ne ga Shaikh Ibraheem Zakzaky. 

An gudanar da nadin sarautar ne a fadar masarautar Zazzau da misalin karfe 11 na safe .

 Sheikh Sani na cikin mutum bakwai da aka yi wa sarauta a ranar. 

Indai ba a mance ba sama da wata shida ke nan Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris ya baiwa Sheikh Sani takardar tabbatar masa da Sarautar, wanda kuma sai ranar Asabar aka nada shi.

Sauran Sarautun da aka nada a wannan rana sun hada da; Abdullahi Nuhu Bayero (Dan Iyan Zazzau), Avm Bashir Said Gamagira (Wakilin Soron Zazzau), Alhaji Muktar Yusuf Bamalli (Garkuwan Bai Zazzau), Alhaji Shamsudden Ibrahim, (Ubandoman Zazzau), Alhaji Shehu Yero (Makaman Raya kasar Zazzau) da kuma Abdullah Garba Mazadu (Wakilin Dangin Zazzau). 

Post a Comment

0 Comments