'Masu Karamin Karfi Na Cikin Mawuyacin Hali A Nijeriya'


A halin yanzu rahotanni na nuni da yadda ake fuskantar hauhawan farashin kayayyakin masarufi da ba a taba ganin irin sa ba a shekaru 15 da suka gabata.

Rahoton Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda farashin abinci ya karu da kashi kusan  kashi 27 cikin dari a watan Fabarairu kawai na shekarar bana.

Hukumar auna ci gaban tattalin arziki ta kasa ta bayyana irin tashin gwauron zabin da farashin kayyakin masarufi ke yi a kasar yanzu haka, inda ta kuma bayyana cewa masu dan karamin hali na cikin wani mauyacin hali.

Daya daga cikin sashen da ya fi jin jiki a wannan  yanayi shi ne bangaren kiwon kaji a cewar wannan hukuma.

Post a Comment

0 Comments