Mukabala Na Nan Daram Da Abduljabbar -Gwamnatin Kano Ga Sarkin Musulmi


Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa zaman mukabala da za a yi da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano tana nan daram sai an yi ba gudu ba ja da baya, inda gwamnatin ta ce shirye-shirye ma ya yi nisa lokaci kawai ake jira. 

Kwamishinan al'amuran addini na Kano, Muhammad Tahar (Baba Impossible) shi ne ya shaidawa gidan Rediyon Freedom Kano, inda ya ce matsayar Jama'atu Nasril Islam a karkashin Sarkin Musulmi suma jinta suka yi kamar yadda kowa ke ji amma ba su samun sakon JNI din ba. 

Baba Impossible ya ce zama na nan saboda su ba a karkashin kungiyar suke ba. 

Post a Comment

0 Comments