Mun Bi Umurnin Kotu Wajen Dakatar Da Mukabalar Abduljabbar Da Malaman Kano -Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje


 
Gwamnan jihar Kano,  Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai yi biyayya ga umurnin kotu wajen dakatard a mukabalar da za a yi da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan shari'a na jihar, Barista Musa Abdullahi Lawal. Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin ba za ta karya umurnin kotu ba musamman idan aka yi duba da cewa kotun na da hurumin bayar da umurnin. 

Inda ya tabbatar da cewa yanzu babu batun mukabala a ranar Lahadi kamar yadda rahoton gidan Rediyon Freedom Kano ya tabbatar. 


Karanta labarin nan; YANZU-YANZU: Ku Dakatar Da Yin Mukabala Da Abduljabbar -Umurnin Kotu Ga Gwamnatin Kano


Post a Comment

0 Comments