Na’Abba Zai Jagorancin Gangamin Korar APC Da PDP A 2023

 

Ghali Umar Na’Abba


Daga Muhammad Farouk

Shugaban tafiyar ‘National Consultative Front (NCFront)’ a jiya sun kaddamar da kwamitin membobi 22 da za su yi hadakar siyasa a karkashin tsohon Kakakin majalisar kasa,  Ghali Umar Na’Abba, inda aka dora musu alhakin ‘tattaunawa da fito da hanyar da za su samar da babban jam’iyya ga ‘yan Nijeriya”. 

Tafiyar ta su wacce ake so ta tabbata zuwa watan Yunin 2021, za su yi aiki 

Membobin mutum 22 din na kwamitin wanda kungiyar NCFront ta ayyana, an ba su aikin tattaunawa tare da fito da nagartacce tsari mai kyakkyawan manufa ta samar da jam’iyyar siyasa ta ‘yan kasa baki daya da za ta tafi da mutane masu ‘yan adamtaka da kuma kungiyoyi masu manufofi kyawawa. 

An kaddamar da kwamitin ne ta hanyar taron da aka gudanar ta Intanet a jiyan, inda aka sanya mutum 12 wadanda yake shugabanni a wadansu jam’iyyun siyasa, sai mutum mutum tara da suke jagorori a wadansu kungiyoyi. 

Babban shugaban NCFront shi ne Farfesa Pat Utomi, shi ne ya kaddamar da kwamitin, inda ya ayyana Ghali Na’Abba a matsayin shugaban kwamitin, sai Cif Raph Okey Nwosu (shugaban jam’iyyar ADC) a matsayin mataimaki, sai Dr. Olu Agunloye (shugaban jam’iyyar SDP) a matsatin Sakatare.

Sauran sun hada da Dr. Osagie Obayuwana (tsohon shugaban NCP); Arch. Ezekiel Nya Etok (tsohon shugaban YDP); High Chief Peter Ameh (tsohon shugaban IPAC da PPA), Dr Tanko Yunusa (shugaban NCP).

Sauran sun hada da Sanata Zainab A. Kure, Rt Hon Jumoke Akindele (tsohon Kakakin majalisar jihar Ondo, Kwamared Issa Aremu (shugaban LP), Cif Precious Elekima (shugabar PLIF), Sanata Folashade Grace Bent da kuma Dr Aisha Salihu Lemu (Shugabar mata) da sauran su. 

Shugabannin NCFront har wala yau sun yi alkawarin cewa ba za su yarda a sake wani zabe a kasar ba ba tare da wani sabon kundin tsarin mulki ba. 

Majiyarmu ta Daily Trust ta labarto cewa kungiyar ta shirya gabatar da wani sabon daftarin kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda Cif Olisa Agbakoba zai jagoranci samarwa. 

Farfesa Utomi ya nemi shugabancin Na’Abba ya yi amfani da dukkanin damar da aka bai wa kwamitinsa da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da sun samar da babban jam’iyya wacce za a gabatar da ita a watan Yunin 2021. 

Na’Abba a jawabinsa na amsar wannan aiki da aka ba shi, ya tabbatar da cewa kwamitinsa zai yi aiki tukuru wajen  zuwa inda za shi wajen kawo daftarin tsare-tsare, kundin tsarin mulki, suna, tambari, take da tsarin shugabanci na sabuwar jam’iyyar siyasar.  


Post a Comment

0 Comments