Nijeriya Ce Kasa Ta Biyu Da Ke Dauke Da Marasa Aikin Yi A Duniya


Nijeriya ta biyu dake dauke da marasa aikin yi a fadin duniya. Kamar yadda Jaridar Bloomberg ta bayyana, inda ta ce an samu karuwar rashin aikin yi a watannin  hudun farkon shekarar 2020.

Nijeriya wacce take dauke da mutum fiye da miliyan 200 a duniya, an bayyana cewa rashin ayyukan yi ya karu daga kashi 27.1 zuwa 33.3 a watannin hudun farkon shekarar 2020 kamar yadda rahoton kididdigar ta kasa, NBS ya tabbatar.

NBS ta ce ta ce an samu raguwar marasa aikin yi daga kashi 28.6 zuwa 22.8, kuma idan aka hada marasa aikin yi da marasa aikin yi mai gwabi a wadannan watanni sun kai kashi 56.1.

A kididdigar da NBS ta saki, ya nuna jihar Imo ce ke dauke da marasa aikin yi mai yawan gaske, inda suka kwashi kashi 56.6, sai jihar Adamawa da kashi 54.89.

“idan aka hada rashin aikin yi da kuma rashin aikin yi mai gwabi, jihar Imo na da kashi 82.5, sai Jigawa da kashi 80, sai Ogun da Sokoto  da kashi 26.2% da 33.7%”.

Bloomberg ta nuna cewa rashin aikin yi ya kai kashi 33.3 a Nijeriya, inda ya zarce kasar Afrika ta Kudu, cikin jerin kasashe 82, sai dai kasar Namibia ce ta daya da kashi 33.4.

Rashin aikin yi a Nijeriya shi ne mafi muni tun bayan da kasar ta fada matsalar rushewar tattalin arziki sau biyu cikin shekara biyar.

-Rahoton Jaridar Dimokuradiyya

Post a Comment

0 Comments