Nijeriya Na Da Hatsarin Zama, Inji Kungiyar Global Terrorism Index

Sakamakon karuwar hare haren 'yan bindiga da matsalolin tsaron da suka mamaye wasu sassan Njeriya, kungiyar dake sanya ido kar ayyukan ta’addanci ta duniya da ake kira Global Terrorism Index ta bayyana kasar a matsayin daya daga cikin mafi hadari wajen rayuwa a fadin duniya.


Rahotan kungiyar na shekarar 2020 da aka gabatar, ya ce an samu karuwar hare haren mayakan boko haram da kashi 25, yayinda kashe kashen da 'yan bindiga keyi ya karu da kashi 26 sabanin wadanda aka gani a shekarar 2019.

Rahotan kungiyar ya ce kasashen da ke gaban Najeriya wajen fuskantar irin wadannan matsaloli a duniya kawai sun hada da kasar Iraqi da Afghanistan wadanda suma ke fama da matsalolin tsaro.

Kungiyar ta Global Index ta ce tsakanin watan Fabarairun shekarar 2020 zuwa watan Fabarairun bana an kasha mutane 2,769 a Jihar Barno kawai, yayin da garkuwa da mutane domin karbar diyya ya karu tsakanin kungiyoyin Yan bindiga a cikin shekaru 5 da suka gabata.

Kungiyar ta ce tsakanin bara zuwa bana an biya kudin da ya kai Dala miliyan 18 a matsayin diyyar mutanen da akayi garkuwa da su.

Global Index ta ce yayin da matsalar tsaro ya zama jiki a Najeriya, arewacin kasar yafi fuskantar radadin wannan matsala, saboda hare haren book haram da harin Yan bindiga da rikici tsakanin makiyaya da manoma da masu garkuwa da mutane da kuma rikice rikicen dake da nasara da kabilanci da addini.

Rahotan kungiyar yace kananan yara ma basu tsira ba wajen fuskantar wadannan matsaloli, ganin yadda a yankin arewa maso gabas ake kashe su da sace su da cin zarafin su da kuma amfani da su a matsayin sojojin haya, duk da matsalolin da suke fuskanta na rashin muhalli da kuma rashin abinci mai gina jiki.

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla yara 4,000 aka kasha tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 a Najeriya, yayin da Hukumar UNICEF ta ce daga cikin mutane kusan miliyan 2 da suka rasa muhallin su, kashi 60 yara ne kanana.

Rahoton RFI Hausa

Post a Comment

0 Comments