PRP Ta Ki Amincewa Ta Yi Maja Da Sabuwar Jam’iyyar Da Za A Kafa

 

Jam’iyyar ‘Peoples Redemption Party (PRP)’ ta tabbatar da cewa ba za ta hade da wata kungiya ko wata jam’iyyar siyasa ba domin kafa wata sabuwar jam’iyya domin fuskantar zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai a Abuja a ranar Laraba, inda ya kara da cewa duk da an gayyaci jam’iyyarsa, amma ba su amsa gayyatar ba.

Bello ya ci gaba da cewa wadansu jam’iyyun sun hade wuri guda domin kafa babban sabuwar jam’iyya, sai dai ya ce bai sani ba ko haduwar a kan kyakkyawan manufa aka yi ta.

Ya nemi gwamnatin tarayya da ta fitar da tsari mai kyau da zai magance matsalar taron kasarnan.

Bello ya ce akwai karancin jami’an tsaron ‘yan sanda a kasarnan, akwai bukatar a kara su domin inganta tsaron kasar. `

 

Post a Comment

0 Comments