Rashin Hakuri Akan Titunan Jihar Kano Daga Salihu Tanko Yakasai


Akullum na fita unguwa akan titunan Kano, fargaba nake har na isa inda zani ko na dawo gida, saboda yanayin gajen hakurin masu ababan hawa da suka hada da manyan motoci, kananan da na Adaidaita da ma babur, kowa sauri yake kamar masu gudun mutuwa. 

Idan kana kokarin tsallaka titi musamman ma a manyan tituna kamar namu Hadejia Road, ko irin su Zaria Road, ko su Ibrahim Taiwo Road da makamantan su, wahalar da zaka sha ba kadan ba ce, musamman a lokacin da yamma ta yi, sanda kowa ke kokarin komawa gida. Wani zubin masu tahowa,  'daga maka kafa na sakan biyar za suyi, ka samu ka tsallaka titi amma da zarar ya hango ka, toh sannan zai kara wuta dan mugunta. Irin haka kuma idan da tsautsayi sai dai kaga an yi hadari kamar yadda ta faru da ni a kwanakin baya, sanda wani mai mashin ya manno a dari ni kuma zan tsallaka titi tare da iyali na gaba daya a cikin mota, ya afka mana, sai da muka je asibiti da shi da 'da na sun ji ciwo. 

Banda wannan kuma, haka zaka ga ana gajen hakuri idan aka zo mahada wato Junction, musamman inda babu jami'an KAROTA, 'dan hakurin da wani zai ka wuce sai ya ki yarda, ya cuso kan abin hawan sa, kuma idan akai rashin dace daga nan hanya ta kulle, shi bai wuce ba, kai bai barka ka wuce ba, kaga sauri ya haifi nawa kenan. 

Saboda haka ne, naga ya dace nai kira ga al'ummar jihar Kano, dan Allah mu koyi hakuri, mu dinga yiwa juna uzuri akan titunan mu, Allah Ya yi wa Jihar Kano albarka ta yawan mutane, wannan ba karamin arziki bane, dan haka kar mu bari yawan mu ya zama jidali, ya sa mu kullum a cikin kunci da damuwa. Duk sanda ka 'daga kafa ka bawa wani dama ya wuce, ina kyautata zatan sai ya shi maka albarka, ya gode ma. Sannan kai kuma kai tunanin lokacin da kake kokarin tsallaka titi amma kai ma an hana ka dama, ya kake ji a ranka? Idan kuma ka samu wani bawan Allah ya barka ka wuce, shi ma ya kake ji a ran ka? Irin haka zata sa mu dinga yiwa juna adalci, kuma ana samun raguwar yawan hadari da sauran su. 

Ba mu da jihar da ta fi Kano, arewa na alfahari da Kano, har makotan Najeriya kamar su Nijar na alfahari da Kano, mu hadu mu inganta ta domin samun ci gaba da ingantacciyar rayuwa. Nagode.

Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.
8th March, 2021.

Post a Comment

0 Comments