'Yan fashin daji aƙalla huɗu ne suka mutu bayan wata fafatawa da suka yi da dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojan Nijeriya a Jihar Katsina, a cewar mai magana da yawun rundunar kamar yadda rahoton BBC ya labarto.
Wata sanarwa da Birgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar a yau Asabar ta ce dakarun sun yi nasarar kashe miyagun ne yayin wani samame ranar Alhamis a garin Marina na Ƙaramar Hukumar Safana.
Wasu 'yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, a cewar sanarwar, yayin da dakaru suka ƙwace babura da kuma bindigar AK-47 guda biyu.
Ya ce an ga tawagar 'yan bindigar ce É—auke da shanun da suka sata kuma nan take sojoji suka far musu a kusa da garin Batsari zuwa Runka.
A gefe guda kuma, dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Puff Adder ta kashe ɗan fashi ɗaya tare da ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47 a Ƙaramar Hukumar Kanƙara.
Kakakin 'yan sandan Katisna, SP Gambo Isa, ya ce dakarunsu ne suka far wa miyagun bayan sun kai wa ƙauyukan Matsiga da Masaku hare-hare a daren Juma'a, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu.
0 Comments