Sanata Okorocha Zai Gina Makarantun Almajirai A Wasu Jihohin Arewa


A yunkurinsa na shawo kan matsalar da ta ke tattare da almajiranci a Najeriya, Sanata Rochas Okorocha zai gina makarantun tsangaya na zamani.

Jaridar Katsina Post ta labarto cewa Sanatan na Imo ta yamma zai gina wadannan makarantun ne a wasu jihohi shida na yankin Arewacin kasar nan.

Tsohon gwamnan jihar Imo zai yi wannan kokari ne ta hannun gidauniyarsa ta ‘Rochas foundation’ wanda ta dade ta na irin wannan namijin aiki.

Abdulmalik Mahmud ya bayyana wannan ne a lokacin da jagoran Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Ahmad Tijjani Nyass ya kai masu ziyara a garin Bauchi.

Mahmud ya ce jihohin da za su samu wadannan makarantun almajirai na zamani sun hada da ita kan ta Bauchi da Kano, Katsina, Yobe, Borno, sai Zamfara.

Wadannan makarantu za su hada karantun addini musamman Al-qur’ani da karatun zamani na boko.

Gidauniyar Rochas Fondation ta ce akwai alaka mai karfi tsakanin jahilicin da ake fama da shi a kasar nan da kuma rashin tsaro da ya dabaibaye al’umma.

Shugabar makarantar Rochas foundation college ta jihar Bauchi, Misis Sarah Johnson, ta bayyana cewa an kafa makarantun ne domin ‘ya ‘yan talakawa.

Kwanakin baya kun ji cewa fitaccen shehin darikar tijjaniyyah na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ja kunnen gwamnoni a kan batun almajiranci.

Da yake karatun tafsirinsa na shekarar bara, Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga gwamnonin yankin Arewacin Najeriya su daina tsangwamar almajirai.

Post a Comment

0 Comments