Shin Da Gaske Gwamnati Ta Kara Kudin Man Fetur?


 

Daga Muhammad Farouk

Hukumar lura da farashin man fetur, PPPRA a ranar Alhamis ta bayyana cewa akwai yiwuwar farashin man fetur a gidajen mai ya kai naira 212.11 duk lita daya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a sabon farashin mai din da ta fitar na watan Maris bisa lura da farashin da ake shigo da man fetur din.

Ta ce abin da ake kashewa a duk lita na man ya kai N4.81 a yayin da hukumar lura da tasoshin ruwa wato NPA ke karbar N2.49 a duk lita, ita kuma NIMASA na karbar N0.23 duk lita, sai Jetty Thru suna sanya N1.61 duk lita, sai kuma ana karbar N2.58 duk lita na 'Storage charge', sannan ana kashe N2.17 duk lita a matsayin 'finance cost', wanda hakan ke sanya man ya iso a N189.61 duk lita.

Takardar ta ci gaba da cewa ana siyan man a N4.03 duk litra, sannan ana sanya masa N1.23 a matsayin 'administration charge,' a duk lita, alawus din zirga-zirga (NTA) na daukar N3.89 duk lita. Sai kuma farashin ''Bridging Fund' na daukar  N7.51 duk lita, sai dauko shi daga ruwa yana daukar da aka fi sani a turance da 'Marine transport average (MTA)' a N0.15 duk lita. 

Hukumar ta PPPRA ta ce wannan bayanan ba yana nufin za a yi karin kudin man fetur din bane ga 'yan Nijeriya, inda ta ce karin kudin man fetur din ana yin shi ne a hukumance.

Hukumar dai ta saki wadannan bayanan ne a watan Janairu da Fabarairu, kuma har yanzu a hukumance ba a yi karin kudin man fetur din ba ga 'yan Nijeriya.

Tuni kamfanin man fetur na Nijeriya wato NNPC ya je ba za a yi karin kudin man fet ur din ba a watan Maris.

 

 

Post a Comment

0 Comments