Shugaba Buhari Zai Tafi Landan A Duba LafiyarsaShugaban Najeriya Muhammadu zai tafi birnin Londin da ke kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.


A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce shugaban na Najeriya zai tafi birnin London ranar Talata domin ya ga likita.


Sanarwar, wadda mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya sanyawa hannu ta ce Shugaba Buhari zai koma Najeriya a mako na biyu na watan Afrilu mai zuwa.


"Shugaban kasa zai soma ganawa da jami'an tsaro da safe, daga bisani zai yi tafiyar," in ji Mr Adesina.


Shugaba Buhari zai yi tafiyar ne a yayin da kungiyar likitoci ta sha alwashin soma yajin aiki ranar 1 ga watan Afrilu saboda rashin kayan aiki da isasshen albashi.


Rahoton BBC HAUSA

Post a Comment

0 Comments