Shuka Bishiyoyi A Jihar Kano -Daga Salihu Tanko Yakasai


Jihar Kano na bukatar bishiyoyi domin dalilai da dama da suka hada da kiwon lafiya ta hanyar tsaftace iskar da muke shaka, da maganin kwararowar hamada, da samar da inuwa, da dai sauran su, haka kuma a addinance ma idan ka shuka bishiya ba karamin lada zaka samu ba. 

A daidai wannan lokaci, shine lokacin da yafi dacewa na yin shukar bishiya, yan watanan kadan kafin faduwar damuna. Idan ka shuka ta a yanzu, saiwar ta zata kama kasa ta kuma saki, yadda da damuna ta zo sai dai kaga ta mike ta na girma, wanda kuma kamawar ta sosai a lokacin damuna zai rage dawainiyar kula da ita da za kayi, dan haka ka samu sauki. 

Ni a karan kai na, tare da hadin gwiwar wani amini na Alhaji Sani Tasiu Maitangaran mun shuka bishiyu a layin gida na, kuma Alhamdulilah yanzu sum girma ana mora. Na yi niyyar shuka su, sai ya nemi alfarmar shi zai siya ni kuma na kula da su, kuma hakan aka yi, yanzu Alhamdulilah sun girma. Irin wannan yana da kyau, domin samun lada da inganta rayuwar mu. 

Gwamnatoci da dama sun sha yunkurin shuke shuke, amma ba'a samun nasarar mikewar bishiyun saboda rashin kulawa ta musamman, har su girma. Haka ma kungiyoyi da dama suma suna kokarin shuka bishiyoyi, kamar kungiyar Panacea Charity wadda a shekarar da ta gabata ta shuka bishiya kusan dubu goma, kuma a wannan shekarar ma zasu sake guda dubu goma a Kano. Amma inda gizo yake sakar shine dole sai al'ummar jihar Kano sun dauke ragamar kula da bishiyun nan sannan zaa samu nasarar cimma buri.

A nan ne nake kira ga al'ummar jihar Kano, da su daure su ga sun shuka bishiyoyi a kalla koda iya kofar gidan ka ne ko wajen sana'ar ka. Kuma ko da kwaya daya ce. Amma ka tabbatar ka samar mata kariya kar dabbobi ko yara su karya ta, sannan kuma a dinga bata ruwa har tsayawar damuna ta mike da kanta. Idan al'ummar jihar Kano suka rungumi wannan tsari hannu bibiyu, toh in Sha Allah cikin kasa da shekaru kalilan zaka ga jihar Kano ko ina kore, birni da karkara. 

Da fatan wanda ya karanta sakon nan zai isar wa da wani, kuma wanda ya ji sakon nan zai dau nauyin shuka daya tak kafin faduwar damuna. Inada mabiya shafin nan nawa na Facebook mutum dubu dari uku (300,000) wanda akasarin su yan Kano ne, da ace mutum dubu bari (100,000) daga ciki zasu yi aiki da shawarar nan kadai, toh da an samu bishiya dubu dari daya a jihar Kano cikin kankanin lokaci. Ina fata wannan shawara ta zama hanyar silar kawo chanji a jihar Kano, a bangaren rashin bishiyu a jihar mu abar alfaharin mu. Nagode.

Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.
Kano Tree Planting Campaign.

Post a Comment

0 Comments