Labarin dake shigowa MADOGARA a halin yanzu shi ne tsohon Shugaban Makarantar kwalejin Ilimi ta gwamnatin Tarayya dake Zariya, Dr. A A Ladan ya rasu.
Makusantan Marigayin sun shaida mana cewa za a yi Jana'izarsa ne da misalin karfe biyu da rabi a gidansa dake Unguwan Iya a cikin Birnin Zariya.
"Lallai an yi rashin bawan Allah mutumin Kirki. Muna addu'a Allah ya jikansa da Rahama. Allah ya Gafarta masa dukkan kurakuransa", inji wani bawan Allah.
0 Comments