Wadanda Suka Fitar Da Bidiyon 'Dollar' Za Su Ji Kunya -Ganduje


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu yana da hannu wajen fitar da faifan bidiyon dake nuna shi yana sanya daloli a cikin aljihun babban rigarsa.


Ganduje ya bayyana faifan bidiyo a matsayin yarfe da ake neman bata masa suna, kuma tuni aka kaddamar da bincike akai domin gano wadanda suke da hannu a ciki.


Gwamnan ya ce bidiyon karya ne tsagoranta domin babu wani abu makamancin haka da ya taba faruwa, yayin da yake bayyana shi a matsayin yunkuri ne kawai na hana shi takarar neman wa’adi na biyu wanda tuni ya samu nasara akai.

Jaridar Daily Nigerian ce ta wallafa hotan bidiyon wanda ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Nijeriya, yayin da Editan Jaridar Malam Jaafar Jaafar ya kuma je Majalisar dokokin Kano domin kare shaidun da suke da shi dake tabbatar musu da labarin.

Tuni gwamnatin Jihar Kano taje kotu dangane da lamarin.

Post a Comment

0 Comments