Yadda Aka Yi Wa Shugaba Buhari Da Osinbajo Basillar Rigakafin Korona

 Daga Muhammad Farouk 

An yi wa Shugaba kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo allurar rigakafin Korona.

Su duka biyun an musu allurar rigakafin ta AstraZeneca ne a babban dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Asabar. Inda aka haska yadda ake musu allurer kai tsaye a gidajen Talabijin na Nijeriya.


Likitocin suma sun yi allurar a kansu a gaban membobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya. Likitoci uku da wata ma’aikaciyar jinya ne suka fara yin allurar a ranar Juma’a.

Kuma yanzu haka, ana shirye-shiryen tura allurar rigakafin zuwa duk fadin kasar nan sannan kuma gwamnoni sun sha alwashin kaddamar da yin allurar a talabijin kai tsaye don karfafawa mutane gwiwar yin rigakafin.

Sai dai kuma, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce ba zai yi allurar ba saboda yana cikin koshin lafiya.

Bello, wanda ya ce Kogi na da matsalolin da suka fi dacewa a magance fiye da yin rigakafin cutar ta korona wadda ya bayyanata a matsayin wata dabara.

 


Post a Comment

0 Comments