Yadda Mahara Suka Kashe Mutum Daya Da Garkuwa Da Dama A Jihar Katsina

Daga Wakilinmu

Rahotanni na nuni da yadda mahara suka kai wa wani mutum mai suna Abubakar Ya'aqub hari har gonarsa suka kashe shi. 

Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Litinin a garin Yankara dake karamar Hukumar Faskari a jihar ta Katsina. 

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa an kashe Malam Abubakar ne a yayin da ya je gonarsa kilomita daya tsakanin gonar da cikin garin Yankara, inda 'yan bindigar suka bude masa wuta, suka kashe shi nan take. 


Tuni aka yi Jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. 

Shekara guda ke nan da garin Yankara ya fara fuskantar barazanar 'yan ta'adda. Inda yanzu hare-haren ya dawo sabo fil, kamar waccan shekarar. 

Rahotanni sun nuna cewa bayan maharan sun kashe Abubakar Yaqoub da safe, da yammacin jiyan sun dira a Unguwar Barau sun bude wuta kan jama'a. 

Sannan sun shiga Unguwar Mai Dawa-Yankara duk a jiyan, sun kashe mutum ɗaya da safe, sun yi garkuwa da uku da yamma, Maza biyu masu sana'ar yankan ice, da Mace ɗaya Mai Tsohon Ciki!

Post a Comment

0 Comments