Yadda 'Yan Bindiga Suka Sake Sace Dalibai Da Malamai A Kaduna

 


Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce gungun ‘yan bindiga sun kai har ikan wata makarantar firamare dake kauyen Rama a karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka sace malamai da dalibai.

Wadanda suka shaida aukuwar tashin hankalin sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da malaman da kuma daliban ne kan babura fiye da 10.

Wasu mazauna yankin sun shaidawa majiyoyin kafafen yada labarai da dama a Najeriya cewar, barayin sun afkawa makarantar Firamaren ta kauyen Rama ne, da misalin karfe 9 na safe, a daidai lokacin da dalibai ke kokarin shiga dakunansu na daukar karatu.

Sace daliban Firamaren na Rama dake Birnin Gwari na zuwa ne yayin da ake cikin jimamin daliban kwalejin horas da ayyukan raya Gandun Daji dake jihar ta Kaduna da wasu ‘yan bindigar suka sace wadanda suka saki bidiyon dake nuna daliban tare da bukatar biyansu diyyar naira miliyan 500 kafin su sake su.

Wasu daga cikin daliban da suka yi magana a bidiyon wanda ke nuna 'yan bindigar dauke da bindigogi sun bukaci gwamnati da ta taimaka wajen kubutar da su ba tare da amfani da karfi ba.


-Rahoton RFI Hausa

Post a Comment

0 Comments