Yadda Yanayin Rayuwa Ke Sanya Iyaye Mata Su Maida 'Ya'yansu Jarinsu


Daga Safiyanu Ladan Da Bilkisu Ibrahim 

'Ya'ya amana ce wanda Allah ya daura mana mai nauyin gaske, saboda haka wofantar da su da rashin ba su kyakkyawar kulawa cin amanar Allah ne. Allah (SWT) ya ce 'ya'yanku da dukiyoyinku fitina ce a gare ku, amma idan ku ka yi hakuri, ku ka kauda kai, ku ka yi gafara lallai Allah mai gafara ne kuma mai jinkai.
Akasarin iyaye mata dake zaune a Karkara da Birane talauci da rashin samun tsayayyen mijin da zai biya musu bukatunsu da na 'ya'yansu, ya sa suka maida 'ya'yansu jarinsu.


Namiji shi ne zai daukewa mace da 'ya'yanta dukkan bukatunsu domin su kasance cikin farin ciki, annashuwa da walwala ya kuma zame musu garkuwa daga dukkannin abin da ya tunkaro su ko zai fada musu.


Yayin da namiji ya zama ba zai iya gudanar da hakan ba, tabbas rayuwar 'ya mace tana cike da hatsari, firgici, kaskanci da kuma kunci, domin guje ma haka ya zama wajibi ga namiji ya tashi tsaye haikan domin ya dauki nauyin da ya hau kansa.

Duba da yadda rayuwa ta zama yanzu kowa yana son ya ji dadi ba tare da ya wahala ba, hakan yasa da yawa daga cikin mazaje suka bar wa mata ragamar tafiyar da harkokin gida. Zaka samu sau da yawa matan ne suke fafutikar nemo abin da za a ci da sauran abubuwan da ake amfani da shi a gidan, ita ce sabulun wanka dana wanki, man shafawa, sutura, kayan kwalliya, audugar kunzugu, kayan daki idan bikin 'yarta ya tashi da kuma akwatin auren danta.


Irin wannan halin rayuwa da suka tsinci kansu yasa suka jefar da duk wani mataki na tarbiyyantar da 'ya'yansu musamman mata. Sun tura su tallace-tallace, gidajen aiki da kuma barinsu su yi mu'amala da mazaje wadda ba ta dace ba.


Irin wannan mu'amala da mata suke yi da maza za ka ga yarinya ba ta sana'ar komai amma da wayar da ta kai naira dubu hamsin (50, 000) ko fiye da sunan saurayinta ne ya siya mata. Kuma daga mahaifin har mahaifiyar sun san cewa saurayi ba zai sayi waya ta 50, 000 haka kawai ba, amma saboda sun san ta hakan suke samun abin masarufi ba su isa su hana yarinyar wannan mummunan mu'amala da saurayinta ba balle su tuhume ta yadda aka yi har ya bata waya.

Sannan kuma wani abin da zai baka takaici shi ne yadda zaka ga mahaifin don rashin sanin ciwon kai da kishi, a wurin yarinyar zai dunga karbar abin da zai kashe yana tinkaho ai yarinyarsa mai farin jini ce shi yasa samari suke mata hidima. Allah wadaran naka ya lalace. 

Iyaye da yawa sun sakarma yara ciyar da su. Misali 'yan kauye za su tura yara talla da ribar tallar za a ci abinci har a yi kayan daki, ba maganar makarantar Boko balle Islamiyya.
Su ma 'yan Birni suna na su, za ka ji da an yi sallama da yarinya, mahaifiyar ko mahaifin za su ce je ki ki samo mana ko na Koko ne. Don girman Allah ka ji irin wannan lalacewa. To suna nufin haka nan za ta samu na kokon ba tare da komai ya faru ba?

Su kuma mutanenmu na kauye daga talla aka samu ci gaba zuwa aikatau gida-gida domin a cewarsu yafi riba, duk wata su je su amshi kudinsu ba tare da la'akari da tarbiyyar gidan ba, koma me za a yi ma yarinya oho. Kudi nake samu, su kuma suna ganin kudi suke biya don haka sun dauke su bayi.

Ka ga su 'yan Birni akwai samfurin yadda suke na su, za su dauki yarinya akai ta gidan Kawu ko abokin Baba ko makwabci, kuma an san gidan ba tarbiyya, amma sai a kauda kai, a yi biris. Da yawansu ai musu ciki, wajen zubarwa su mutu. Wasu su zama 'yan Shaye-shaye, su dauko miyagun dabi'u.

Duk hakan na faruwa ne saboda mahaifin da mahaifiyar ba za su iya daukar nauyin abin da suka haifa ba. Wanda wallahi idan ka ga abin da yake faruwa gwara mahaifiyar ta dauki tallanta aka ya fi ta ba 'yarta. Mahaifiya ta yi aikatau, wankau ya fi ki tura 'yarki.

Ai da Manzon Allah (SAW) ya ce ku hayayyafa don na yi alfahari da ku ranar gobe kiyama, nagartattun 'ya'ya ake nufi wadanda za su zama masu ceton iyayensu daga azabar Ubangiji.

Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ku nemi duniya kamar ba za ku mutu ba, haka ku nemi lahira kamar yanzu zaka mutu. Wannan cutarwa ne, ku ku kwanta a gida ku tura yara nemo muku abin da za ku ci. Akwai hisabi fa, wanda idan kuka alkinta su, ku ka ba su ilmi, su za su zame muku jigo ko garkuwa duniya da lahira.


Duba ga haka ya zama wajibi ga hukumomi su shigo cikin wannan lamarin domin ganin iyaye sun kauce wa abin da zai jefa yaransu cikin halaka. Hukumomi su samar da doka da zai tursasa ma duk wani wani magidanci daukar nauyin da ya hau kansa. Ka da su kuskura ko da wasa su daurama yara ragamar tafiyar da al'amuran gidansu musamman yara mata.


Malamai da shuwagabannin alumma su tashi tsaye wajen wayar da kam mutanenl, su fa'ida da alfanun daukar nauyin iyalansu. Sannan kuma hukumomi su samar da abubuwan da za su rage ma mutane kuncin rayuwa da kuma za su saukaka musu wurin neman abin da za su rufama kansu da 'ya'yansu asiri. 

Allah ya datar damu ya bamu ikon sauke nauyi da ya hau kanmu. Allah ya masa gudummawa. Amin.


Zaku iya tuntubar marubutan a; 
Safiyanu Ladan 
uncledoctor24@gmail.com
07069145252

Post a Comment

0 Comments