'Yan Bindiga Na Son Mazauna Kauye A Katsina Su Biya Harajin Miliyan 10 Idan Suna Son Zaman Lafiya


Daga Muhammad Farouk

Bayan harin da aka kai a kauyen Kakumi dake karamar Hukumar Bakori a jihar Katsina, 'yan bindiga sun nemi 'yan kauyen su biya naira miliyan 10 domin kare kawukansu daga hare-hare a gaba kamar yadda kafar watsa labaran Blueinknews ta labarto. 


'Yan bindigar sun nemi hakan ne ta wayar tarho bayan da suka kira mutanen kauyen a ranar Asabar. 


Daya daga cikin al'ummar garin a zantawarsa da majiyarmu, ya labarta cewa 'yan bindigar sun tabbatar da cewa biyan kudaden ne kawai zai kare mutanen kauyen daga hare-haren 'yan bindigar. 


Idan ba ku manta ba, a ranar Juma'a ne dai da misalin karfe 7 na dare, 'yan bindigar suka kai hari a kauyen Kakumi dake karamar Hukumar Bakori a jihar Katsina, inda suka kashe mutum uku da kuma raunata da dama. 

 

Post a Comment

0 Comments