‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Bakwai A Kaduna –Rahoton Gwamnati

 


An kashe mutum bakwai da dama sun raunata sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyakun kananan hukumomin Igabi, Giwa da kuma Chikun dake jihar Kaduna. 

Kwamishinan lura da tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa ya fitar.

Samuel Aruwan ya ce an kashe mutum hudu wanda ya hada da; Wada Sulaiman, Amiru Saidu, Yusha’u Mohammadu da Osama Abdulwahab, a kauyen Gangi dake karamar Hukumar Igabi. 

Ya ci gaba da cewa har wala yau 'yan bindigar sun kona gidaje uku a yayin farmakin da suka kai, inda ce kuma mutum biyu sun samu rauni daga harbim bindiga. Kuma tuni aka kai su asibiti. 

Ya kara da cewa; "an kuma sace shanu 20 na mutum biyu a kauyen. Sannan a wani labarin kuma, 'yan bindiga sun kai hari kauyen Marke dake karamar Hukumar Giwa, suka kashe wani mai suna Rabi'u Haruna", inji Aruwan. 

Rahoton na gwamnatin ya tabbatar da harin da 'yan bindiga suka kai a kauyen Kuriga dake karamar Hukumar Chikun, inda suka kashe mutum biyu a titin Buruku dake hanyar karamar Hukumar Birnin Gwari. 

Wadanda aka kashe sune; Ibrahim Yahu Birnin Gwari da Haruna Usman. Sai Mansur Dada, ya samu rauni, inji rahoton gwamnatin. 

Post a Comment

0 Comments