'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 13 A Sabon Farmakin Da Suka Kai Jihar Sakkwato

 

'Yan bindiga sun kai hari daren a jiya a kauyen Tara da ke karamar hukumar Sabon birni, inda suka kashe mutane 13, suka kuma jikkata wasu guda 7.

Dagacin garin Tara, Mainasara Muhammad Tara ya ce maharan sun yi nasarar kwashe dabbobi da dama, yayin da suka kona rumbunan ajiye abincin su.

Mai Garin ya ce 'yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 11.58 na dare, ta wata barauniyar hanya, saboda gadin da matasa ke yiwa hanyoyin shiga garin kamar yadda RFI Hausa suka tabbatar.

Muhammad Tara ya ce sun dade basa iya bacci a garin saboda yawan hare-haren 'yan bindigar, abin da ya sa suke raba kan su domin sanya ido.

Mai Garin ya ce wannan shi ne karo na biyu da 'yan bindigar ke kai musu hari a cikin watanni biyu, kuma a harin farko sun yi asarar dabbobin da yawan su ya kai 200.


Post a Comment

0 Comments