‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku A Kauyen Jihar Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
 

Daga Wakilinmu 

Wadansu ‘yan bindiga sun dira a kauyen Rurum dake karamar hukumar Rano ta jihar Kano da misalin karfe 1 na daren Talata, inda suka yi awon gaba da matar dan kasuwa, Alhaji Yusuf Jibrin.

Wani mazaunin kauyen ya tabbatarwa da majiyarmu ta Sahelian Times da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindiga sun bude wuta ne wanda hakan ya yi sanadin kashe mutane uku da sace Alhaji Yusuf Jibrin da matarsa, Hajiya Asabe Jibrin, inda daga bisani aka sake mijin.

Ya kuma kara da cewa an harbi dan uwansa wanda daga bisani ya rasu da yammacin ranar Laraba a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, sauran kuma mutanen wanda ya hada harda na wani tsoho wanda ya tsere daga hannunsu suna karbar magani.

Ya ci gaba da cewa; hukumomin tsaro ba su isa wurin da lamarin ya auku ba har sai bayan ‘yan bindigar sun kammala kaddamar da hare-harensu.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya kara da cewa ‘yan bindigar sun sace mutum biyu amma sun kubutar da mutum daya a yayin da suke bibiyar yadda za su kubutar da dayan.

Harin na zuwa kasa da mako daya da kaddamar da sabon kwamishinan ‘yan sanda a jihar.

 

Post a Comment

0 Comments