'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Al'ummar Fulani A Kaduna


Daga Muhammad Farouk 

Wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe shugaban al'ummar Fulani na Doka dake karamar Hukumar Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Lawal Musa wanda aka fi sani da Alhaji Maijama'a. 
 
Kwamishinan al'amuran tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin ya auku ne a daren Litinin. 

Ya kara da cewa an yi wa Alhaji Lawal Musa mummunan kisa a gaban iyalinsa. 

Kwamishinan ya ce:  “Alhaji Lawal Musa shi ne shugaban a Doka general area dake karamar Hukumar Kajuru wanda yake aiki tukuru da sauran shugabannin al'umma wajen tabbatar da zaman lafiya da kawo ci gaba mai dorewa a yankin". 

Kwamishinan ya ce an kashe Alhaji Musa ne a cikin motarsa a yayin da yake tare da Yayansa, Alhaji Gide Musa, inda 'yan bindigar suka zo suka bude musu wuta. 

“Alhaji Gide Musa ya tsira da raunuka, inda 'yan bindigar suka cafke Alhali Musa suka yi masa kisan gilla". 

Post a Comment

0 Comments