Daga Wakilinmu
Wasu 'yan bindiga sun far wa Unguwar ma'aikatan hukumar kula da filayen jirgin sama ta Nijeriya (FAAN) da ke Jihar Kaduna, inda suka sace mutum 11.
Mai magana da yawun FAAN, Henrietta Yakubu, ta ce 'yan bindigar sun shiga Unguwar ce da safiyar yau Asabar, kamar yadda ta shaida wa TheCable
"Sun É—uki ma'aikatanmu kusan tara da kuma iyalansu a unguwar," in ji ta.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan fashin sun shiga unguwar ne bayan sun karya shingen wayar da ya raba filin jirgin da kuma gidajen ma'aikatan. Sai dai ba a samu rahoton ko an rasa rai ba.
Mazauna unguwar sun bayyana cewa ƙarar harbe-harben da maharan suka yi ta sa wasu sojoji da ke kusa suka mayar musu da martani.
Sai dai daga baya sun gudu da mutanen da suka sata, waÉ—anda jumillarsu ta kai 11.
0 Comments