‘Yan Majalisar Tarayya Sun Talauce –Kakakin Majalisar

 

Benjamin Kalu, Kakakin Majalisar


Kakakin majalisar Tarayya, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa ‘yan majalisar Tarayya sun talauce, shiyasa ba sa iya gudanar da ayyukan da ke kawukansu yadda ya kamata. Inda ya nemi a kara yawan kudaden da ake bai wa ‘yan majalisar.

Dan majalisar na jam’iyyar APC daga jihar Abiya wanda ya kuma kasance Kakakin majalisar, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, inda ya ci gaba da cewa; “na fada da farko, ina kara kuma jaddada, ba na kuma tsoron sake fada”, inji shi.

Sun kara da cewa; “wannan shi ne gaskiya, har sai ‘yan Nijeriya sun gane cewa kudaden da ake bai wa ‘yan majalisar wajen gudanar da majalisar a lokacin da Dala Daya take naira 180, yanzu ya yi kasa ma da yadda ake bayarwa a baya”, inji Kalu.

 

 

Post a Comment

0 Comments