YANZU-YANZU: Ku Dakatar Da Yin Mukabala Da Abduljabbar -Umurnin Kotu Ga Gwamnatin Kano


Daga Wakilinmu

Gidan Rediyon Freedom dake Kano ya labarto cewa; wata kotun Majistare mai lamba 12 dake gidan Murtala ta dakatar da gwamnatin daga shirya mukabala tsakanin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano. 

Umurnin kotun ya biyo bayan karar da wani Lauya mai suna Ma'aruf Yakasai ya shigar gaban kotun, inda ya nemi kotun ta dakatar da mukabalar. 

A yayin zaman kotun a yau Juma'a, Mai Shari'a Muhammad Jibril ya bada umurnin dakatarwar har zuwa 22 ga watan Maris din nan da ake ciki. 

Post a Comment

0 Comments