YANZU-YANZU: ‘Yan Bindiga Sun Kone Kauyen Ruwan Tofa Kurmus A Jihar Zamfara

 

                                                            Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle

  

Wadansu ‘yan bindiga sun kona kauyen Ruwan Tofa dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka yi kuma garkuwa da mutum 60, wanda mafi yawan wadanda aka sace din mata ne da kananan yara.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun kuma tsere da kudaden jama’ar kauyen, tare da kuma harbin mutum daya wanda yanzu haka yake karbar magani a asibiti.

Wannan harin na zuwa ne kwana biyu da ‘yantar da dalibai mata fiye da 200 na makarantar gwamnati ta mata dake Jangebe.

 

Post a Comment

0 Comments