Yariman Zazzau Alhaji Mannir Ya Zama Madakin Zazzau


Daga Aqeel Abdulkadir  

A yau Juma'a 5 ga watan Maris din 2021, Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya nada Alhaji Mannir Jafaru  a matsayin sabon Madakin Zazzau, inda yanzu ya tashi daga Yaiman Zazzau zuwa Madakin Zazzau.

Bikin nadin an takaita zuwan mutane saboda kariya daga yaduwar cutar korona, inda aka yi taron da misalin karfe 11 na safe . Bayan kammalawa sabon Madakin da sauran jama'arsa suka hau motoci zuwa gidansa dake G.R.A a Sabon Garin Zariya.

Idan ba a mance ba, Alhaji Mannir Jafaru na cikin wadanda aka kawo cewa zai zama sabon Sarkin Zazzau watannin baya da Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu. 

Sarautar Madaki a masarautar Zazzau nada girman gaske, domin ita ce Sarauta mafi girma da ake baiwa dan Sarki. 

Mannir Jafaru da ne ga Sarkin Zazzau Jafaru Dan Isiyaku daga gidan sarautar Barebari. 

Ga wasu kadan daga cikin hotunan taron da Wakilinmu ya aiko mana da shi. 

Post a Comment

0 Comments