Za A Fafata Tsakanin Atletico Madrid Da Real Madrid A Mako Na 26

 

A gobe Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci Atletico Madrid, domin buga wasan hamayya a gasar La Liga fafatawar mako na 26.

Kungiyoyin biyu sun fuskanci juna fiye da sauran masu buga La Liga tun daga kakar 2013/14, kuma wasa na 30 da za su kece raini a tsakaninsu.

A karawar farko a La Liga da za su fafata a bana ranar 12 ga watan Disamba, Real ce ta yi nasara a gida da ci 2-0.

Atletico ce ke jan ragamar teburin La Liga na bana da maki 58 da kwantan wasa daya, Real Madrid mai maki 53 tana ta uku a teburin na gasar Spaniya.

Cikin wasa 29 da suka kara tun daga 2013/14 sun hadu a La Liga sau 15 da karawa a Champions League karawa shida.

Sauran fafatawar sun kara a Copa del Rey karo hudu da wasa uku a Spanish Super Cup da gumurzu daya a European Super Cup.

Tun daga wasan European Super Cup a Agustan 2018, Real ta yi nasara a wasannin hamayya shida, kuma ba a doke ta ba.

Ciki har da wanda Real Madrid ta lashe Spanish Super Cup a Jeddah a Janairun 2020, bayan da ta yi nasara a kan Atletico a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Post a Comment

0 Comments