A Shirye Izala Ta Ke Ta Karbi Sheikh Jingir A Kan Tafarkin Sunnah Na Gaskiya -Bala Lau


              Shaikh Abdullahi Bala Lau

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce daga yanzu ahlussunnah ba za su bari wani ya fito haka kurum ya na zagin sahabbai a kowace jiha a Najeriya ba. Imam Bala Lau da ke gabatar da fadakarwa a masallacin marigayi Sheikh Alhassan Sa'id Adam a Jos jihar Filato, ya nanata yabo ga gwamnati da al'ummar don dakatar da wani mai fakewa da yin wa'azi ya na cin mutuncin sahabbai da taba janibin manzon Allah.

Sheikh Bala Lau ya nuna farin ciki yadda malamai a Kano da sauran sassa su ka hada kai fiye da yawanci  lokuta a baya wajen kare sunnah. Shehun malamin bai kammala ba sai da ya nuna takaicin yadda Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ki bin hadewar JIBWIS kamar yadda ya nemi a yi, ya na mai cewa har yanzu a shirye Izala ta ke don sake karbar Sheikh Sani Yahaya da jama'arsa a kan bin tafarkin sunnah na gaskiya.

Iman Bala Lau ya ce tun taron na Ahlusunnah COAN da a ka yi a Legas ya kan aikawa Sheikh Sani Yahaya takardar gayyata amma bai taba mutunta gayyatar ba, inda shi kuma Sheikh Sani bai taba gayyatarsa zuwa wa'azi ba ko sau daya.

Tuni malamai da dama da su ka yi karatu mai zurfi a jami'ar musulunci ta Madina irin su Saifuddeen Yakubu Musa su ka gabatar da wa'azi da a masallatai da dama, inda aka karkare a masallacin marigayi Sheilkh Alhassan Sa'id Jos. Filato na daga manyan cibiyoyin kungiyar da ke da mabiya a ciki da wajen Najeriya har da nahiyar turai da sauran sassan duniya kamar yadda shafin Jibiwis Nigeria ya labarto. 


Post a Comment

1 Comments

  1. Ya zaiyi da jalo jalingo da Yan qungiyarsa dake zagin annabi da Ali bn Abi Talib,sunce iyayen annabi na wuta wai Ali ba musulmi bane a wajensu...

    ReplyDelete