Zan Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci A Jihar Zamfara –Gwamna Matawalle

Gwamna Bello Mohammed Matawalle 

Daga Muhammad Farouk 

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya ce gwamnatinsa ta kusan fallasa ko su wane ne ke daukar nauyin ta’addanci a jihar. 

Gwamnan ya  bayyana hakan ne a yayin da yake karbar ziyarar da Sarakunan gargajiya na jihar a karkashin jagorancin Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed Anka wanda suka kai wa gwamnan ziyara a gidan gwamnati domin jajanta masa bisa sace dalibai mata sama da 300 na makarantar Sakandaren gwamnati dake Jangebe a ranar Juma’ar da ta gabatar. 

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamantinsa kiris ya rage ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar, amma ya ce ba zai yi hakan ba sai bayan an ‘yanto dalibai matan da aka yi garkuwa da su. 

Gwamnan ya kara da cewa: “da zarar mun ‘yanto dalibai mata da aka yi garkuwa da su, zamu fallasa wadanda suke haddasa ayyukan ‘yan bindiga a jihar Zamfara domin ganin mun kawo karshen matsalar a jihar”, ya tabbatar.

Ya bayyana sulhun samar da zaman lafiya da gwamnatinsa ta bullo da shi a matsayin hanyar kawai da ta rage wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar, inda ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a karkashin gwamnatinsa da su dauki wannan hanyar a matsayin hanyar kawo karshen matsalar. 

A na shi jawabin a madadin Sarakunan da suka kai wa gwamnan ziyarar, Sarkin Anka Alhaji Anka ya ce sun zo gidan gwamnatin ne domin jajantawa gwamnan jihar Zamfara din, iyayen dalibai matan da aka sace bisa wannan ibtila’in da ya auku. 

Sarkin ya bayyana lamarin a matsayin wani abin tashin hankali da rashin tausayi, inda ya tabbatar da cewa za su yi dukkanin abin da ya kamata su yi wajen ganin tattaunawar sulhun da gwamnatin ta fito da shi a jihar a karkashin gwamnan ya haifar da da mai ido domin ci gaban jihar da samar da dawwamammen zaman lafiya. 


Post a Comment

0 Comments