A Cikin Awa 24 An Kashe jami'an Tsaro 21 A Sassan NijeriyaA jiya Talata 28 ga watan Afrilun 2021, labarai marasa dadin ji sun auku a sassan Nijeriya na kai hare-hare da kashe jami'an tsaro da ke bai wa kasarnan kariya.

Jaridar MADOGARA ta tattaro wasu daga cikin hare-haren nan da aka kai cikin awa 24, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 21. 

1. A jihar Kebbi wadansu'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda guda 8. 

2. A jihar Imo an kashe 'yan sanda guda biyu. 

3. A jihar Ribas kuwa ana kashe sojoji guda biyar. 

4. Inda a jihar Binuwe kuma aka kashe 'yan gudun hijira guda 7. 

5. A jihar Ebonyi kuwa, an cinnawa babbar Kotun Tarayya wuta ne. 

6. An tabbatar da cewa Boko Haram ta kwace karamar hukuma daya a jihar Neja. 

7. An kuma kashe da dama a wadansu kauyukan jihar Katsina. 

Post a Comment

0 Comments