A Kul Dinku Da Zuwa Nijeriya -Gargadin Amurka Ga 'Yan Kasarta


Gwamnatin Amurka ta gargadi jama’ar kasar da su kaucewa tafiya Nijeriya saboda laifuffukan da suka shafi ayyukan ta’addanci da tashe tashen hankula da garkuwa da mutane da kuma fashin teku.

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafin ta ya bayyana cewar Jihohin Borno da Yobe da arewacin Adamawa na fama da ayyukan ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yayin da matsalar garkuwa da mutane kuma ta yi kamari a Jihohin Bauchi da Gombe da Kaduna da Kano da Katsina da kuma Zamfara.

Sanarwar ta ce Jihohin dake gabar ruwa irin su Akwa Ibom da Bayelsa da Cross River da Delta da kuma Rivers na fama da matsalar manyan laifuffuka da garkuwa da mutane da kuma fashin teku.

Post a Comment

0 Comments