A.A Rano Ya Rabawa Mutanen Hadejia Buhun Shinkafa Dubu Biyu


Daga Abubakar M Tahir

Fitaccen dan Kasuwarnan A.A Rano ya aike da buhunan Shinkafa guda dubu biyu ga al'ummar Masarautar Hadejia wanda ya saba bayarwa a duk shekara.

Tallafin da ake badawa ta hannun abokinsa Umar Kaka Ya samu bayin Allah dake da karamin karfi bayan da ake tantancewa gami da rabon katin shedar amsar Shinkafa.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata ne aka fara wannan rabon inda aka bai sa mutum 200, haka ma ranar Alhamis aka ba ma mutum 1000, a yau Kuma Alhamis aka cika sa sauran 800.

Wakilinmu ya tabbatar mana da cewa; mutane da yawa sun sami wannan tallafin wanda yake gabatarwa duk shekara albarkacin watan Ramadana.

Post a Comment

0 Comments