Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abin Da Ya Sa Na Tsaya Takarar Kansila A Jam'iyyar APC -Honorabul Muhammad Auwal

Daga Muhammad Farouk Honorabul Muhammad Auwal Danjuma ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar Kansila ne a jam'...Daga Muhammad Farouk

Honorabul Muhammad Auwal Danjuma ya bayyana cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar Kansila ne a jam'iyyar APC bayan tattaunawa da 'yan'uwa da abokan arziki, iyalai da kuma masu ruwa da tsaki a Harkar siyasa, shugabannin al'umma da kuma kwarin guiwar da yake da shi. 

Honorabul Danjuma har wala yau ya ce burinsa na ganin ya taimakawa al'umma da bunkasa walwalarsu yana daga cikin dalilan da ya sanya yake neman kujerar Kansila a karkashin Jam'iyyar APC. 

Honorabul Danjuma ya tabbatar da cewa ba ya fito ne domin ya yiwa al'umma dadin baki ko alkawarukan da ba zai cika ba, amma yana mai tabbatarwa da al'ummar yankinsa cewa idan aka zabe shi, zai tabbata da ya bunkasa walwalar al'umma baki daya. 

Honorabul Muhammad Auwal Danjuma ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya fitar na sha'awarsa na tsayawa takara da yammacin jiya Juma'a. 

Inda ya karkare da cewa bai fito takarar domin ya rika zargin wasu ba, amma a maimakon zarge-zarge zai tabbata da ya yi aikin a zo a gani wanda za a yaba; "mai fafutika ba shi ne wanda ke korafin cewa wannan kogin ya yi datti ba, a'a shi ne wanda zai yashe dattin kogin kafin korafi", ya lurantar. 

Honorabul Muhammad Auwal Danjuma dai na neman kujerar Kansila ta gundumar Jushi ne dake karamar Hukumar Sabon Garin Zarya a jihar Kaduna a karkashin Jam'iyyar APC mai mulkin jihar. 


No comments