Akwai Yiyuwar Ba Za A Biya Albashin Ma'aikata Ba A Watan Mayu


Jaridar Kakaki Hausa ta labarto cewa; Kamfanin Mai na NNPC ya aikewa da Babban Akawun ƙasar nan Takardar cewa kwabo ba za su bayar ba a Matsayin haraji a wannan watan ba, abunda ke nuna cewa harajin da aka saba bayarwa ayi Kasafin Kudin wata wata a rabawa Tarayya, jihohi da ƙananan Hukumomin ƙasar nan ya samu tasgaro.

A takardar da Shugaban Kampanin na NNPC Mele Kyari ya aikewa babban akawun yayi bayanin cewa harkar biyan tallafin kudin Man Fetur ya Laƙume kudaden da ya kamata a ce sun baiwa Gwamnatin Tarayya a Matsayin harajin da ake bayarwa domin a rarraba duk ƙarshen wata.

“A cewar sa kimanin N111,966,456,903.74 za su cire daga abinda aka samu na riba daga watan Aprilun shekarar 2021 wanda ya kamata a ce an sanya a Asusun Gwamnatin Tarayya domin watan Mayu 2021.”

Takadar mai ɗauke da kwanan watan 26 ga watan Aprilu zuwa ga Babban Akawun na ƙasa tace  Kampanin na NNPC ya samu ƙaracin haraji ne na N111,966,456,903.74 a watan Fabrairu dalilin yadda aka samu tataccen Man Fetur wanda zai iso ƙasar nan akan kudi N184 duk lita ɗaya maimakon N128 duk lita kamar yadda aka saba

Ya kuma danganta haka da rashin samun Matsaya akan farashin Man Fetur din tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƴan Kungiyar ƙwadago 

Tunda farko dai Kyari ya bayyana cewa Kamfanin ba zai cigaba da iya daukar Nauyin biyan tallafin Man Fetur ba inada ya bayyana cewa farashin Man Fetur zai iya kasancewa tsakanin N211 zuwa N234 kowace litre. 

Haka yake nufin cewa masu Amfani da Man Fetur basu biyan ainahin farashin Man wani ne a wani wuri yake cika masu cewa Mr Kyari.

Dama dai ƙasar nan tana dogara ne da harajin Kampanin Man Fetur na NNPC wajen samu Kudaden shigar ta sai kuma Harajin da ake kar'ba daga Kampanoni na Ƴan kasuwa da kuma Hukumar tattara haraji ta ƙasa.

Post a Comment

0 Comments