Allah Na Fushi Da Buhari, Inji Fasto Mbaka

 


Babban Malamin Cocin ‘Adoration Ministry’, dake jihar Enugu, Fr Ejike Mbaka, ya shawaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka akan mulkinsa domin kuwa Allah na fushi da shi. 

Mbaka, wanda ya kasance magoyin bayan shugaba Buhari a yayin zaben 2015 ya nemi shugaba Buhari da ya sauka ko kuma ‘yan majalisa su tsige shi. 

Fasto Mbaka ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a Cocinsa dake Inugu, inda ya ce kuskure ne shugaba Buhari ya ci gaba da yin shiru duk da halin kashe-kashe da kasar ta fada a ciki. 

“na san mutane za su ce Mbaka shin ba ka yi addu’a ga Buhari ba, shin Samuel bai zabi Saul ba? Me kake cewa n? Ni ne Ubangijin Buhari? Allah ya halicce shi, ‘yan Nijeriya suka yarda da shi saboda ya yi wani abin kirki a wadansu lokutan, amma yanzu me zai sanya mutane su rika mutuwa?” ya tambaya. 

Fasto Mbaka ya ce Allah zai tambayi ‘yan Nijeriya me yasa suke kuka? “muna kuka ne saboda shugabanninmu sun ci amanar mu, sun kuma gaza. Da a ce wayayyar kasa ce, ya zuwa yanzu da shugaba Buhari ya sauka a mukamainsa. Ku fada wa duniya cewa ni ne na fada, abubuwan da yake faruwa a kasarnan a yanzu, ya kamata shugaba Buhari ya sauka”, inji shi. 


Post a Comment

0 Comments